Wednesday 25 October 2017

An shawarci Matan Arewa Sa Suyi Koyi Da Dabi'un Rahma Sadau

  Unknown       Wednesday 25 October 2017

Wata gamayyar kungiyoyin matan dake daukacin jahohi 19 na Arewacin Najeriya sun shawarci dukkanin matan dake a yankin na Arewacin Najeriya da suyi koyi da kyawawan halayen jarumar nan ta fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau.
Gamayyar kungiyoyin dai sun yi wannan kiran ne jim kadan bayan sun kammala taron su da suka sabayi a lokaci lokaci inda kuma suka nuna sha'awar ta su fili karara ga halayen na jarumar da suka bayyana cewa masu kyau ne kuma abun sha'awa.

Diranigist.blogspot.com  dai ta samu cewa matan sun shawarci daukacin matan Arewar da su rike sana'ar duk da suke yi sosai ba tare da damuwa da cece-kucen da jama'a za su rika yi masu ba tamkar dai yadda jarumar ta ke cikin yi

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kungiyar masu shirya fina-finan na Hausa a baya sun dakatar da jaruma Rahma Sadau daga yin fim saboda abunda suka kira saba dokar su da ta yi yayin da ta rungumi mawaki a cikin wata waka da suka yi.

logoblog

Thanks for reading An shawarci Matan Arewa Sa Suyi Koyi Da Dabi'un Rahma Sadau

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment