Wednesday 25 October 2017

Babu Wani Bambanci Tsakanin Mulkin Buhari Da Jonathan — Inji Auwal Musa Rafsanjani

  Unknown       Wednesday 25 October 2017

"Babu Wani Bambanci Tsakanin Mulkin Buhari Da Jonathan — Inji Auwal Musa Rafsanjani
Wasu masu fafutika a Najeriya sun soki kamun ludayin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari kan yadda yake tunkarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar, suna f idan ana batun yaki da cin hanci da rashawa, babu bambanci tsakanin gwamnatinsa da ta tsohon Shugaba Goodluck Jonathan."

Masu sukar lamarin shugaban kasar dai na kafa hujja da wasu bincike da aka gudanar na zargin wasu jami'an gwamnati da aikata almundahana, amma shugaban kasar ya kawar da kansa.
Har ila yau, sun ba da misali da rashin daukar matakai bayan ya karbi rahoton binciken sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar Mista Babachir David Lawal.

Da kuma batun daraktan hukumar leken asiri ta kasar NIA, Ayo Oke tare da wasu jami'an gwamnatin kasar da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Auwal Musa Rafsanjani, wakili a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International ya shaida wa BBC damuwarsu

logoblog

Thanks for reading Babu Wani Bambanci Tsakanin Mulkin Buhari Da Jonathan — Inji Auwal Musa Rafsanjani

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment