Thursday 26 October 2017

'Bayan watanni biyu shugaba Buhari na cigaba da aiki daga gida

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Har yanzu shugaban kasa Buhari na cigaba da aiki daga gida


- Watanni biyu kenan da dawowar shugaban kasar daga jinya da yaje a birnin Landan


- An aika wasika ga masu magana da yawun shugaban kasar kan yaushe zai dawo ainahin ofishin sa


Watanni biyu bayan dawowar shi daga jinya a asibitin Landan, jinya da ba a bayyana ba, shugaba Muhammadu Buhari yana ayyuka ne daga gidan shi dake cikin fadar shugaban kasa, a babban birnin tarayya Abuja.


Bayan kwanaki biyu da dawowar shugaban kasar daga hutun jinya da ya tafi na tsawon kwanaki 103, ya rubuta wa majalisan dattawa wasika, yanda kundin tsarin mulkin kasa ta kayyade, ya bayyana dawowar shi kasa da komawar shi bakin aiki a ofishin shi dake fadar shugaban kasa dake Abuja.


Amma daga baya kakakin shugaban kasar sun rubuto cewa zai cigaba da aikin sa daga ofishin sa na gida saboda wasu yan gyare-gyare da za'ayi.


Hakan ya janyo cece-kuce da dama a wancan lokacin.


Duk da haka, bayan watanni biyu, shugaban ya cigaba da jigila tsakanin ofishin shi dake gidan shi da sabon babban dakin taro dake manne da ofishin shi inda yake karban baki.


Fadar shugaban kasa bata bayyana har zuwa yaushe za a kammala gyare-gyaren ba.


An aika wa lambobin wayoyin masu magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina da Garba Shehu wasika, fadan shugaban kasa bata gabatar da amsa kan al’amarin ba cikin gaggawa.

“Barka da maraice ranka ya dade. A watan Agusta, an fada mana cewa shugaban zai dunga aiki daga gida saboda gyara da kamfanin Julius Berger ke gudanarwa a ofishin shugaban. Jaridar Guardian zata nuna ra’ayi kan tabbacin lokacin da shugaban zai fara gudanar da aiki a ofishin shi. Mun gode ranka ya dade. Yawan gaisuwa,” jaridar Guardian ta rubuta a sakon wayar salula.

Amman da tsakan dare Shehu, ya amsa kamar haka: “Babu sashin doka ko tsarin kundin mulkin da aka saba. Dukkannin gine gine dake fadan shugaban kasa ofishi ne kuma gida ne ga shugaban. Yana da damar amfani da kowace bangaren fadar a matsayin ofishi muddin yana gudanar da ayyuka.”

logoblog

Thanks for reading 'Bayan watanni biyu shugaba Buhari na cigaba da aiki daga gida

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment