Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki stohon shugaba Shehu Shagari kan fitar da shinkafa waje
- Ya ce gwamnatin Shagari ta dakile kokarin da kasa keyi na ganin ta samar da wadatacciyar shinkafa
- Obasanja ya kuma jinjina wa mai kamfanin shinkafar ta Hyst Global Business Limited, Mista Biodun Olanaja
A ranar Alhamis din da ta gabata, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsohon shugaban kasa Shehu Shagari, akan yadda ya dakile kokarin kasar nan wajen samar da wadatacciyar shinkafa da har za ta iya fitarwa kasashen ketare.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da jawabai akan kaddamar da kamfanin Shinkafa na Okun a babban labiraren sa dake birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Tsohon shugaban kasar wanda ya bayyana cewa, sauran kiris Najeriya ta wadatar da kanta da Shinkafa a shekarar 1979, kafin ya sauka daga kujerar shugabancin kasar nan a lokacin da yake mulkin soja, wanda sakamakon rashin daidaiton gwamnatoci da kuma manufofin siyasa, ya sanya gwamnatin Shagari ta yi watsi da tsare-tsaren da ya assasa.
Ya ce wannan watsi da Shagari ya yiwa manufofin sa ya yi sanadiyar juyin juya hali a harkar noma ta kasar nan, wanda wannnan yana daya daga cikin matsaolin da kasar nan take fuskanta wajen rashin samun daidaito a tsakanin manufofin gwamnatoci.

Gwamnatin Shagari ta kawo wa Najeriya nakasu a harkar noman Shinkafa – Obasanjo.
Obasanja ya kuma jinjina wa mai kamfanin shinkafar ta Hyst Global Business Limited, Mista Biodun Olanaja, inda ya ce da za a samu makamancin Olanaja 100 a kasar nan to da kuwa kasar ba ta tsaya a wadatar da kanta shinkafa ba, domin kuwa sai an fitar da shinkafa kasashen ketare.
Obasanjo ya kara da cewa, akwai bukatuwar bankunan kasar nan da su saukaka matsin bayar da bashi ga manoma wanda yin hakan zai taimaka kwarai da aniyya wajen habaka harkar noma a kasar nan.A na shi jawabin Olanaja ya bayyana cewa, tabbas Obasanjo ya cancanci lambar yabo, inda ya ce manufofin da gwamnatin sat a tanadar game da harkokin noma sun taimakawa kamfanin ya kai matakin da yake kai a yanzu.
No comments:
Post a Comment