Thursday 26 October 2017

Abun da Allah ba zai ta ba yi wa Najeriya ba - Dogara

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Kakakin majalissar Wakilai Yakubu Dogara ya halarci taron adu'o'i a Abuja


- Yakubu Dogara ya ce gyaran Najeriya ya rataya a wuyan Najeriya ne kadai


- Dogara yace rashin grimama al'adu yana daga cikin manyan kalubale da duniya ke fuskanta a yanzu


Kakakin majalissar wakilai, Rt.hon Yakubu Dogara ya ce ba da malai’ku Ubangiji ya gyara kasar Israila ba “saboda haka Allah ba zai turo mala’ika ya gyara mana Najeriya ba.”


Dogara ya ce gyaran Najeriya ya rataya a wuyar yan Najeriya ne kadai.


Kakakin yayi wannan jawabin ne a lokcin da ya halarci taron adu’o’I a safiyar yau Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja.


Abun da Allah ba zai ta ba yi wa Najeriya ba - Dogara

Dogara ya ce rashin girmama al'adu yana daga cikin manyar kalubale da duniyar ke fuskanta a yanzu.


Dogara ya kara da ce wa babu yadda za ayi kasa ta cigaba idan babu tsoron Allah a zukatar al’ummar ta.

“Kowace kasa ta na da na ta irin matsalolin, Ubangiji muke so ya sauko daga sama yayi mana gyara?

“Ubangiji mu ke son ya turo mana malaiku daga sama sun yi mana gyara? Tunda Allah bai yi wa kasar Isra’ila haka ba, ba zai ta ba yi ma kasar Najeriya haka ba.

“Mu da kan mu za mu gyara kasar mu da taimakon UbangijI,” inji Dogara.


logoblog

Thanks for reading Abun da Allah ba zai ta ba yi wa Najeriya ba - Dogara

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment