Friday 27 October 2017

Gwamna Okorocha yace Shugaba Buhari ba ya tafiya da matasa

  Unknown       Friday 27 October 2017

- Gwamnan Jihar Imo ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari


- Shugaban Gwamnonin na APC yace ana yi babu matasa


- Gwamnan yace dole a fito da tsari domin agazawa samari


Mun samu labari daga Jaridar Daily Post cewa Gwamna Rochas Owelle Okorocha ya soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari.


Rochas Okorocha tare da Shugaba Buhari


Shugaban Gwamonin Jam’iyyar APC a kasar yace Shugaba Muhammadu Buhari ba ya tafiya da matasa a Gwamnatin sa. Gwamnan yake cewa dole Gwamnatin Tarayya ta fitowa Matasan kasar da wani shiri na musamman da zai taimaka.


Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin wani mai ba sa shawara a kan harkokin matasa a Jihar Imo Mr. Kenneth Emelu a wani taro da Hukumar NOA mai wayarwa ‘Yan kasar kai ta shirya a Babban Garin Jihar Imo na Owerri a makon nan.

A cewar sa dai Matasa ba su jin dadin yadda abubuwa ke wakana a kasar ganin yadda ake yi ba da su ba. Mista Emulu yace dole Gwamnatin Jihohi ma su rika sauraron kukan Matasa a Kasar.

logoblog

Thanks for reading Gwamna Okorocha yace Shugaba Buhari ba ya tafiya da matasa

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment