Friday 27 October 2017

An yi yunkurin hana Saraki da Dogara ganawa da Shugaba Buhari

  Unknown       Friday 27 October 2017

An yi yunkurin hana Saraki da Dogara ganawa da Shugaba Buhari


- Masu gadin Fadar Aso Villa sun nemi Saraki su fito daga motar su


- Hakan ne ya jawo kai-kawo kafin su samu ganin Shugaban kasar


Labari daga Jaridar Premium Times ya kai gare mu cewa wata ‘yar takaddama ta faru a jiya da dare a Fadar Shugaban kasa.


Shugaban kasa tare da manyan Majalisa a Villa


Jami’an da ke gadin Fadar Aso Rock sun hana Shugabannin Majalisa shiga yayin da su ke neman ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Masu gadin su nemi Bukola Saraki da Yakubu Dogara su fito daga cikin motar su ta bas.


Ko da dai Shugabannin Majalisar su ka ki yin hakan sai aka hana su izini wucewa zuwa kofa ta gaba, daga nan ne aka nemi su juya mota su koma kimanin karfe 8:00 na dare. Nan ne fa Shugaban Ma’aikatar Fadar Abba Kyari ya shiga maganar.

Abba Kyari ne ya koma ya dawo da su Bukola Saraki bayan sun koma gida kamar yadda mu ka samu labari wanda daga nan ne su ka gana da Shugaban kasar har su ka ci abincin dare tare da Shugaba Buhari da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.

logoblog

Thanks for reading An yi yunkurin hana Saraki da Dogara ganawa da Shugaba Buhari

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment