Friday 27 October 2017

Taron NEC: Mu na nan a kan bakar mu Inji Jam’iyyar APC

  Unknown       Friday 27 October 2017

Jam’iyyar APC tace tana kan bakan ta game da gangamin ta


- A jiya mu fara jin kishin-kishin cewa an daga babban taron


- Jam’iyyar mai mulki tace babu abin da ya canza a halin yanzu


Mun samu labari a jiya cewa Jam’iyyar APC ta musanya maganar cewa ta dage babban taron ta da ta shirya yi kwanan nan.


Jam’iyyar APC ta fara shiryawa zaben 2019


A jiya idan ba a manta ba kun ji daga bakin mu cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta daga taron ta na Majalisar Zartarwa. Sai dai yanzu mun ji daga bakin Jam’iyyar cewa babu abin da ya canza a game da shirin wannan taron na kwanan nan.

Mr. Bolaji Abdullahi wanda shi ne Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC ya bayyana cewa rahoton ba gaskiya bane kuma Jam’iyyar za tayi taron da ta shirya a karshen wannan watan. Za ayi taron ne a Ranar 30 da 31 ga watan nan na Oktoba.

Bola Abdullahi ya bayyana cewa abin da mamaki ace an dage taron don kuwa shi bai samu labari ba. A iya sanin sa, yace manyan Jam’iyyar za su zauna kamar yadda aka tsara.


logoblog

Thanks for reading Taron NEC: Mu na nan a kan bakar mu Inji Jam’iyyar APC

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment