Friday 27 October 2017

Kungiyar Shi’a tayi Allah Wadai akan hare-haren da ‘yan sanda su kai a jihohin Kaduna da Sokoto

  Unknown       Friday 27 October 2017

A ranar Lahadi 20 ga watan Oktoba da ta gabata, kungiyar ‘yan Shi’a ta Najeriya ta gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Arewacin kasar nan domin kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tabi umarnin da babbar kotun tarayya ta zartar shekara kusan guda kenan, akan ta saki shugaban ta Sheikh Ibrahim El Zakzaky daga daurin da ta yi masa ba bisa ka’ida ba.


Kungiyar ta kammala zanga-zangar cikin lumana a sauran birane in banda jihohin Sokoto da Kaduna, sakamakon jami’an ‘yan sanda da suka kai musu hare-hare.

A cikin birnin Kaduna, wani gangami na ‘yan sanda tare da makaman yaki sun tarwatsa taron ‘yan shi’ar daka gudanar da zanga-zanga a babbar hanyar Ahnadu Bello, inda suka bude masu wautar harsashai da barkonon tsohuwa. Sai dai anyi sa’a ba bu rai ko guda da ya salwanta amma mutane da dama sun samu raunuka daban-daban.

A can Birnin Shehu kuma wato jihar Sokoto, jami’an tsaron sun bayyana ne bayan an kammala zanga-zangar cikin lumana, yayin da wasu ma sun fara kama gabansu.

Kungiyar Shi’a tayi Allah Wadai akan hare-haren da ‘yan sanda su kai a jihohin Kaduna da Sokoto

Kungiyar Shi’a tayi Allah Wadai akan hare-haren da ‘yan sanda su kai a jihohin Kaduna da Sokoto

Hakan bai sanya jami’an tsaro sun kyale sub a, domin kuwa sun kai musu hari tare da dugunzuma majalisin cibiyar kungiya, inda suka yi gaba da ababen hawa na ‘yan shi’ar tare da kama wasu daga cikin su.

Diranigist.blogspot.com ta ruwaito daga kungiyar cewa, gwamnatin Buhari bat a dauka rayukan ‘yan shi’a da muhimmanci ba domin kuwa sun tabbatar da haka tun a karon batta da kisan kiyashi na garin Zaria da aka yiwa wasu daga cikin su a shekarar 2015.

Kungiyar ta kuma ce, wannan shi yake nuna cewa gwamnatin Buhari ta nuna adawar ta kungiyar a fili tare da gwamnatocin Kaduna da Sokoto, wanda hakan ya sanya kungiyar take zargin akwai kulle-kulle da gwamnatin keyi domin ta kama wasu manya na kungiyar ta su a ranakun jajaiberin tattakin da suka saba gudanarwa a duk shekara.

Kungiyar ta kara da cewa, hakan ba zai sanya su firgita ko ya girgiza sub a, domin kuwa kasa ya baiwa kowa damar yin addinin sa, kuma tattaki da suka saba gudanarwa a duk shekara ya na cikin ibadun su.



logoblog

Thanks for reading Kungiyar Shi’a tayi Allah Wadai akan hare-haren da ‘yan sanda su kai a jihohin Kaduna da Sokoto

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment