Thursday 26 October 2017

Neman kujerar gwamna a Taraba – Tsohon shugaban APC yayi watsi da tsayar da Aisha Alhassan

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Wani tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar Taraba, Alhaji Hassan Ardo, ya nuna rashin amincewa da tsayawar minista mai kula da harkokin mata, Hajiya Jummai Alhassan, a matsayin mai takaran kujerar gwamna kadai a zabe mai zuwa a 2019, ga shugabancin jam’iyyar a jihar.


Ya bayyana cewa tsayawa takararta yana iya kawo rabuwar kawuna a jam’iyyar a jihar.


Ardo, wanda yake jakadan Najeriya ga kasar Trinidad da Tobago, ya bayyana hakan ne a hira da yayi da jaridar Daily Trust a Jalingo, babban birnin jihar.


Ya fada cewa amincewar kwamiti ta tsakiya na jam’iyyar da Misis Alhassan a jihar ya ci karo da manufar jam’iyyar kan adalci da gaskiya ga dukkan mambobinta.


Neman kujerar gwamna a Taraba – Tsohon shugaban APC yayi watsi da tsayar da Aisha Alhassan


A cewar shi, kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta bayyana karara kan yanda za’a tsayar da dan takara, ya kara da cewa zabukan firamari da yarjejeniya ne karbabbiyar hanya.

Saboda haka, yayi mamakin abinda yasa shugabancin jam’iyyar a jihan ta karkace daga wannan tsarin, inda yake fadin cewa shugabancin jam’iyyar tana nan tana daukan muhimman shawarwari ba tare da hannun masu ruwa da tsaki ba.

Ardo ya ci gaba dda bayyana cewa tashen kungiyar dake kare mutunci mai suna Integrity group ta kafu ne saboda ketare kundin tsarin mulkin jam’iyya da shugabancin jam’iyyar tayi ne a jihar Taraba.


logoblog

Thanks for reading Neman kujerar gwamna a Taraba – Tsohon shugaban APC yayi watsi da tsayar da Aisha Alhassan

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment