Thursday 26 October 2017

Yadda Sufetan 'Yan Sanda ya ba Aisha Buhari wasu manyan motoci

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Sanata Misau ya tona asirin Sufeta Janar na 'Yan Sandan Kasar


- Hamma yace 'Yan Sanda sun ba Matar Shugaban kasa motoci


- Ana dai ta kumfar baki tsakanin Sufetan 'Yan Sanda da Sanatan


Rikicin Sufeta Janar na 'Yan Sanda da Sanatan Bauchi Isa Hamma Misau yana cigaba da canza fasali a yanzu a Kasar.


Sanata ya fasa kwan Matar Shugaban kasa da IGP


Labari ya kai gare mu na cewa Sanata Isa Hamma Misau ya fasa kwan Matar Shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari da Sufeta Janar na 'Yan Sanda Ibrahim K. Idris a Majalisa inda yace an ba Uwargidar Shugaban kasar wasu kyaututtuka.

A cewar Sanatan Matar Shugaban Kasa Buhari ta nemi kyautar motoci daga hannun Jamia'an 'Yan Sanda wanda Ibrahim Idris yayi wuf ya bata manyan motoci kirar jeep na Toyota Prado har 2 duk da ba ya cikin kasafin kudin Hukumar a ranar.

Matar Shugaba kasar ta nemi dogayen motoci ta hannun dogarin ta wanda Sufetan 'Yan Sandan ya aika mata zuka-zukan motoci 2. A cewar sa ma dai akwai wasu badakala iri-iri da Sufetan 'Yan Sandan ya tafka. Yanzu haka dai IG na 'Yan Sandan zai bayyana a Majalisa.


logoblog

Thanks for reading Yadda Sufetan 'Yan Sanda ya ba Aisha Buhari wasu manyan motoci

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment