Thursday 26 October 2017

Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro (hotuna)

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Rahotanni sun kawo cewa yayinda ake zabe a wasu bangarori na kasar Kenya, ana zanga-zanga a wasu kamar su Kisumu sannan kuma ba’a kada kuri’a ko guda ba.


Mafi akasarin titunan dake cikin birinin a toshe suke da duwatsu da tayoyi da suke ci da wuta yayin da masu zanga-zanga ke arangama da jami'an tsaro - suna musayar duwatsu da hayaki mai sa hawaye.


Zuwa yanzu ba’a kada kuri'a ko daya ba a birnin, sannan kuma cikin jami'an hukumar zabe 400 da ake tsammani za su zo, uku ne kadai suka hallara.


Har ila yau babu ko wani akwatin zabe da aka ajiye a runfunan zabe.


Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro


Haka al’amarin yake a unguwannin marasa galihu dake Nairobi inda 'yan adawa ke da rinjaye.

Sai dai a wasu bangarori na kasar ana ci gaba da gudanar da zabe, duk da cewa da alama mutane ba su fito kamar yadda suka fito ba a zaben watan Agusta wanda kotun kolin kasar ta soke.

Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro

Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro

Ana kyautata zaton cewa za a nemi alkalai su yanke hukunci kan ko za a iya amincwa da sakamakon zaben ko kuma a'a.

Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro

Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro

'Yan sanda sun yi arangama da magoya bayan 'yan adawa inda wasu daga cikinsu suke kokarin hana mutane zuwa rumfunan zabe.

logoblog

Thanks for reading Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro (hotuna)

Previous
« Prev Post

1 comment:

  1. Kenya: An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro (hotuna)


    https://diranigist.blogspot.co.ke/2017/10/kenya-yi-dauki-ba-dadi-tsakanin-adawa.html?m=1

    ReplyDelete