Thursday 26 October 2017

'Zargin motoci: Aisha Buhari ta karyata kalaman Sanatan Bauchi

  Unknown       Thursday 26 October 2017

- Sanata Isa Misau ya zargi Matar Shugaban kasa da karbar wasu kyauta


- Aisha Muhammadu Buhari tace abin da Sanatan ya fada ba gaskiya ba ne


- Uwargidan Shugaban tace da motocin hannun ta ta ke amfani har yanzu


Yanzu mu ka samu labari cewa Matar Shugaban kasa Aisha Buhari ta karyata kalaman Sanatan Bauchi Isa Hamma Misau.


Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta karyata Sanata


Sanata Hamma yace Sufetan 'Yan Sanda na Kasar nan ya ba Matar Shugaban kasa motoci manya-manya na Toyota Prado. Dazu Uwargidar Shugaba Muhammadu Buhari tace abin da Sanatan ya fada a gaban Majalisa kwanan nan karya ne.


Matar Shugaban kasar Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta maida martani ne ta shafin ta na Tuwita (@aishambuhari) inda ta bayyana mana cewa har yanzu da motocin hannun ta ta ke amfani ba wasu sababbin daga Jami’an ‘Yan Sanda ba.

Sanata Isa Hamma Misau ya ya zargi Sufeta Janar na 'Yan Sanda Ibrahim K. Idris da ba Uwargidar Shugaban kasar kyauta ne bayan ta nemi karin wasu motoci na musamman domin hidima.


logoblog

Thanks for reading 'Zargin motoci: Aisha Buhari ta karyata kalaman Sanatan Bauchi

Previous
« Prev Post

1 comment:

  1. 'Zargin motoci: Aisha Buhari ta karyata kalaman Sanatan Bauchi

    http://diranigist.blogspot.com/2017/10/motoci-aisha-buhari-ta-karyata-kalaman.html

    ReplyDelete