Thursday 26 October 2017

'Ba'a ga Dambazzau a zaman majalisa na yau ba

  Unknown       Thursday 26 October 2017

Ministan harkokin cikin gida, Lt.-Gen Abdulrahman Dambazau (rtd), bai halarci zaman majalisa wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis ba.

An far taron misalin karfe 11:00 am na safe.

Danbazzau ya kasance daya daga cikin yan majalisan da ake zargi da hannu cikin sake kiran tsohon shugaban hukumar kula da harkokin fansho, Abdulrasheed Maina

Alkalin alkalai na kasa da ministan shari’a, Abubakar Malami, da shugaban ma’aikatun tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita, sun kasance a taron majalisan.




Ba'a ga Dambazzau a zaman majalisa na yau ba


Malami, wanda ya isa harabar taron misalin karfe 10:53 na safe ya tattauna da ministan labarai, Lai Mohammed, ministan ilimi, Adamu, kafin gabatar da taken kasa.

Oyo-Ita ta isa harabar taron misalin karfe 10:54 na safe.

Maina, wanda ya gudu kan zargin naira biliyan N2 da ake yi masa, ya dawo cikin aikin gwamnati ba tare da masaniyan shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shugaban, a ranar Litini ya bada umurnin sauke Maina daga aiki da gudanar da bincike cikin gaggawa kan yanda aka sake kiran shi



logoblog

Thanks for reading 'Ba'a ga Dambazzau a zaman majalisa na yau ba

Previous
« Prev Post

1 comment:

  1. Ministan harkokin cikin gida, Lt.-Gen Abdulrahman Dambazau (rtd), bai halarci zaman majalisa wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis ba.

    ReplyDelete