Thursday 26 October 2017

Ýan daba ɗauke da muggan makami sun far ma Ofishin yaƙin neman zaɓen Sule Lamido

  Unknown       Thursday 26 October 2017

An samu tashin tashina a ranar Laraba 25 ga watan Oktoba yayin da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya kai ziyara ofishin yakin neman zabensa dake jihar Kaduna.


Sai dai isar sa ofishin ke da wuya sai jama’a suka fara dafifi a farfajiyar ofishin, inda aka fara taruwa, wanda hakan ya sanya Lamidon yi musu jawabi, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Ana tsaka da taron sai yan daba dauke da makamai suka diran ma jama’a dake wajen, inda suka tarwatsa taro tare da ji ma muatne da dama raunuka daban daban.

A jawabin nasa, Lamido ya caccaki gwmanatin APC karkashin jagorancin Muhammadu Buhari, inda ya zargeta da gazawa wajen iya salon mulki da tafiyar da kasa.

“Idan an samu zaman lafiya a kasa, za’a samu cigaba mai daurewa. Idan an samu kwanciyar hankali, jama’a zasu zuba jari a kasa, amma a yau Najeriya ta shiga mawuyacin hali, yan Najeriya muna ta cin muruncin junanmu.”

Daga karshe Lamido yace zai farfado da martabar Najeriya idan ya samu damar shugabancin kasa, don kuwa ba zai lamunci matasa su dinga shan wiwi suna daukan muggan makamai ba.


logoblog

Thanks for reading Ýan daba ɗauke da muggan makami sun far ma Ofishin yaƙin neman zaɓen Sule Lamido

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment