Wednesday 25 October 2017

Hotunan motar wani Gwamna data babbake a Legas, wanda darajarta ya kai naira miliyan 44

  Unknown       Wednesday 25 October 2017

- Motar alfarma mallakin Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ta kama da wuta


- Farashin motar ya kai naira miliyan Arba'in da hudu


Wata motar alfarma mallakin Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ta kama da wuta bal bal a jihar Legas a ranar Talata 24 ga watan Oktoba, inji rahoton Daily Trust.


Majiyar diranigist.com motar mai suna G-Wagon kirar Marsandi ta kai naira miliyan 44, ta kama da wuta ne yayin da take kan hanyar zuwa filin tashi da saukan jiragen jihar Legas.




Sai dai an ruwaito gwamnan baya cikinta, kamar yadda Kaakakin gwamnan Lere Olayinka ya bayyana, sa’annan babu wanda ya samu rauni, duk da cewa babu wanda ya san musabbabin faruwar gobarar.

Olayinka ya isar da sakon gadiya daga gwamnan ga mutanen da suka taimaka wajen kashe wutar. Wani bincike da majiyar mu tayi ya bayyana cewa farashin wannan motar ya kai dala 122,440, kimanin N43, 941, 000.


logoblog

Thanks for reading Hotunan motar wani Gwamna data babbake a Legas, wanda darajarta ya kai naira miliyan 44

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment