Wednesday 25 October 2017

'Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki ma'aikatan ungozoma 49

  Unknown       Wednesday 25 October 2017


Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki ma'aikatan ungozoma 49

- Gwamnatin na kokarin farfado da asibitocin gwamnati a jihar

- Gwamnatin ta samar da kayayyakin aikin asibiti ga asibitocin gwamnati a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da daukar ungozoma 49 a cikin kokarin rage rashin samun ma’aikata a yankin kiwon lafiya na jihar.

Ciyaman na ma’aikatar asibiti na jihar, Dakta Nasir Sa’idu ne ya bayyana hakan a taron da aka yi a garin Gusau a ranar Laraba. Ya kuma bada shaidar cewa gwamnatin zata dauki ma’aikata likitoci da nas-nas a kwanan-nan


Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki ma'aikatan ungozoma 49


Dakta Sa'adu ya bayyana cewar ungozoman da gwamnatin zata dauka za a tura su kananan asibitoci na kauyuka ne domin farfado da asibitocin. Sannan ya kara musa wata sanarwa da aka yi a kwanaki na cewa jihar Zamfara na da likitoci 23 ne kacal.

A cewar sa ‘muna da likitoci 149 a karkashin gwamnatin jihar, 89 a asibitin Yariman Bakura da ke Gusau, akwai likitoci 60 kuma da suke aiki a asibitocin cikin jihar.’


Gwamnatin jihar na nan tana samar da kayayyakin ayyukan asibiti a cikin jihar. Asibitoci 21 kuwa tuni an maida su tsarin asibitocin zamani, sauran asibitocin na kananan hukumomin Talata Mafara, Gummi, Shinkafi da Kauran Namoda za a gyara su a maida su na zamani suma a samar da kayan aiki a ciki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


logoblog

Thanks for reading 'Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki ma'aikatan ungozoma 49

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment