Wednesday 25 October 2017

Dalilin Da Yasa Na Bawa Rahama Sadau Shawara Akan Ta Bawa Gwamna Ganduje Da Sarkin Kano Sunusi Hakuri — Ali Nuhu

  Unknown       Wednesday 25 October 2017

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya
kasance mutumin da ya karfafa wa
korarriyar jaruma Rahama Sadau gwiwar
ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar
Ganduje da mai martaba sarkin Kano
Muhammadu Sanusi II hakuri kan
al’amarin da ya kai ga dakatar da ita
daga masana’antar shirya fina-finan Hausa a shekarar bara.

Ku tuna cewa kungiyar kula da ladabtar da masu shirya fina-finai wato MOPPAN ta yanke hukuncin korar jarumar bayan ta bayyana a wani kasetin waka wanda bai dace ba tare da mawakin Jos ClassiQ.

Ali Nuhu wanda yayi magana da jaridar Daily Trust akan wayan tarho yayinda yake shirin barin kasar ya bayyana cewa jarumar ta yanke shawarar bayar da hakuri ne bayan ta gane kuskurenta ya kara da cewa dan Adam ajizi ne.
“ A matsayinmu na manya a masana’antar
shirya fina-finai, hakki ne da ya rataya a
wuyanmu domin kula da na kasa damu
wannan ne dalilin da yasa na jajirce wajen
bada hakurin ta.

“A rayuwa yana da kyau mutun ya gyara
sannan ya bada hakuri a duk lokacin da ya saba. Rahama ta yi jarumta wajen bayar da hakurinta sannan kuma tayi alkawari
bazata sake aikata wannan laifi ba kuma. Ta rubuta wasikar ban hakuri zuwa ga
kungiyar MOPPAN wanda na tabbata a
yanzu haka jami’an kungiyar na tattaunawa aka” cewar Ali Nuhu.

A daren ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, da take magana a wani shirin gidan radiyo mai taken “Ku Karkade Kunnuwan Ku” wanda ake gabatarwa a shahararren gidan radiyo a garin Kano, Radio Rahama, jarumar ta sha alwashin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba.

logoblog

Thanks for reading Dalilin Da Yasa Na Bawa Rahama Sadau Shawara Akan Ta Bawa Gwamna Ganduje Da Sarkin Kano Sunusi Hakuri — Ali Nuhu

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment