Wednesday 25 October 2017

"Yan majalisar dattawa sun taimakawa ma'aikatan jihar Kogi

  Unknown       Wednesday 25 October 2017

- Sanatoci sun bayar da tallafi ga ma'aikatan Jihar Kogi wadda suka kwashe watanni 22 babu albashi


- Sun bayar da buhunan shinkafa 1260 da buhunnan takin noma da wasu kayyayakin


- Sanata Melaye, mai wakiltar Yammacin Kogi ne ya bayyana wa manema labarai


Akalla buhunan shinkafa 1200 ne Sanatoci su ka bayar ga ma'aikatan Jihar Kogi. Dino Malaye, sanata mai wakiltan Yammacin Kogi, ya sanarwa manema labarai a zauren Majalisa, ranar Laraba.


A cewar Malaye, wannan gudummuwa amsa kiran da ya yi wa abokan aikin na sa ne na kawo dauki ga ma'aikatan Jihar da su ka shafe watanni 22 babu albashi. A gudummuwar ta su har da buhunan taki na noma.


Ya kuma ce za su cigaba da taimakawa musamman ganin yadda rashin albashin ya sanya wani ya kashe kan sa. Melaye ya sanar da cewan wasu sanatocin kuma sun yi alkawarin bayar da takin noma.


Sanata Malaye ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya masu akwai-da-niyya da su ma su tallafa wurin rage ma ma'aikatan zafin wahala, a cewar sa, a cikin azababben shedaniyar Gwamnatin Yahaya Bello, Gwamnan Jihar.

Don haka Malaye ya yi kira ga Kungiyar Kwadigo ta Jihar da ta yi tsari mai kyau wurin tafiyar da wannan tallafi ta hanayar da ta dace.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:



logoblog

Thanks for reading "Yan majalisar dattawa sun taimakawa ma'aikatan jihar Kogi

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment