Friday 27 October 2017

'Yan fashi sun bindige wani jigo a jam'iyyar PDP da wasu mutum 4 a jihar Zamfara

  Unknown       Friday 27 October 2017


- Wasu ‘yan fashi da makami sun halaka wani dan jam’yyar PDP a jihar Zamfara

- ‘Yan fashin sun kasha fasinjoji da suke cikin motar, bayan nan suka yashe su

- Direban motan yana kwance a asibitin karamar Hukumar Tsafe yana jinya

A ranar Juma’a ne wasu ‘yan ta’adda da ake zargi sun hallaka wasu mutane biyar tare da wani shahararren dan jam’iyyar PDP Alhaji Abdulhadi Saidu Garkuwan ‘Yan ware a jihar Zamfara
Daga jaridar Daily Trust, mun sami rahoton cewa ‘yan fashin sun tsare kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau tare da harba harsashi kan motocin da suke tahowa.
'Yan fashi sun bindige wani jigo a jam'iyyar PDP da wasu mutum 4 a jihar Zamfara

Diranigistcom ta sami rahoton yadda ‘yan ta’addan sun tsare wasu motoci tare da kasha mutane a cikin motar, bayan na n kuma suka tattare guzurin da mutanen suka yi. Nan suka harbi dan jam’iyyar PDP a wuya bayan da motar su ta afka ma inda ‘yan fashin suka tare.

A hanyar su ta dawowa daga garin Kaduna ne bayan sun kammala wani taro da rashin sanin cewar ‘yan fashin na lambo a kan hanyar . Direban motar ya sha da kyar amma yana jinya a asibitin karamar hukumar Tsafe.
Marigayin Alhaji Saidu ya rasu yana da shekara 38 wandda dan asalin garin Tsafe ne, ya kammala karatun digirin sa a Jami’ar Usmanu Danfodio. Ya dade yana siyasa a karkashin jam’iyyar PDP. Ya mutu ya bar mata daya da yaro guda.

logoblog

Thanks for reading 'Yan fashi sun bindige wani jigo a jam'iyyar PDP da wasu mutum 4 a jihar Zamfara

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment