Friday 27 October 2017

Wani Mutumi yayi wa Matar sa kishiya bayan Matar sa ta ba sa kyautar Miliyan 5

  Unknown       Friday 27 October 2017

Wata Mata ta dafa ruwan kona kan ta da kan ta
- Wata mata ce ta ba Mijin ta kyautar Miliyoyin kudi
- Shi kuma kurum da ya tashi zai ya kara aure nan take
Wannan shi ne abin da Hausawa ke kira ruwan dafa kai inda ta kona kan ta da kan ta kwanaki bayan ta yi wa Mijin ta alheri.

Wannan Matar kamar yadda labari ya zo mana ta ba Mijin ta kyautar kudi ne har Naira Miliyan 5 inda shi kuma ya tattara kudin kurum ya je ya karo amarya. Wannan abun dai ya jawo ce-ce-ku-cen gaske a kafofin sadarwa.

Kamar yadda wanda ta san wannan Matar ta bayyana a shafin ta na Tuwita mai suna Yaxmanda a Ranar Talata tace Matar ta ba Mijin na ta kudin ne daga cikin gadon da ta samu daga Mahaifan ta inda shi kuma ya saka mata da kishiya.

Wasu dai sun soki lamarin inda su kace bai dace ya kara aure da kudin da Matar sa ta ba sa ba. Wasu kuma na ganin tun da ya halatta a addinin Musulunci babu matsala.

logoblog

Thanks for reading Wani Mutumi yayi wa Matar sa kishiya bayan Matar sa ta ba sa kyautar Miliyan 5

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment