Friday 27 October 2017

Fatalwar Gaddafi ta hana tsohon shugaban kasar Faransa sukuni

  Unknown       Friday 27 October 2017


- Tsohon shugaban kasar Faransa Sarkozy na cikin hali ni 'ya su
- Ana tuhumar Sarkozy da kisan gillar da aka yiwa Gaddafi
- Sarkozy yayi bakin jini wurin mutanen Faransa saboda rawar da ya taka a kisan Gaddafi
Tun bayan mutuwar Marigayi tsohon shugaban kasar Libiya, Gaddafi, faransawa suka dorawa Nikola Sarkozy karan tsana har ta kai da yasha kasa a zaben kasar da aka yi a shekarar 2012.
Duk da faduwa zabe da yayi, Sarkozy, yaci gaba da fuskantar matsin lamba daga daga 'yan jarida da lauyoyi, duk dai saboda rawar da ya taka a hambarar tare da kisan Gaddafi.
Fatalwar Gaddafi ta hana tsohon shugaban kasar Faransa sukuni

Tun da fari mutanen Faransa sun hada karfi da karfe domin ganin ya zama wurin zama a gidan yari amma suka gamu da cikasa a kotu saboda rashin kwararan hujjoji.
Yayin da ake tunanin kurar mutuwar Gaddafi ta kafa, kwatsam sai ga shi wasu 'yan jaridar kasar Faransa, Fabrice Arfi da Karl Laske, sun bijiro da wasu jigagan hujjoji, da sukayi shekaru 6 suna tattarawa, na zahiri daga ciki da wajen Libiya da zasu iya nutsar da Sarkozy har abada.
Hakazalika kasashen Afrika guda 15 sun shigar da karar Sarkozy kotun ta'addanci ta duniya wato ICC, suna masu tuhumar sa da aikata laifukan kisan kai, take hakkin bil'adama, da kuma kawo tabarbarewar tsaro a yankinsu.
Ana alakanta duk wannan tarnaki da Sarkozy ke fuskanta da kisan Marigayi Gaddafi.

logoblog

Thanks for reading Fatalwar Gaddafi ta hana tsohon shugaban kasar Faransa sukuni

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment