Friday 27 October 2017

Tir: Hukumar EFCC ta damke wani tsohon kawai a Kaduna

  Unknown       Friday 27 October 2017

Hukumar EFCC tayi ram da wani tsoho da laifi


- Ana zargin tsohon ne da amfani da kudin bogi


- Ba kuma yau tsohon nan ya fara wannan aiki ba


Mun samu labari daga Jaridar Rariya cewa Hukumar EFCC ta kama wani tsoho a Garin Kaduna da ke amfani da kudin karya. Yanzu haka dai ana Kotu inda ake shari’a.


EFCC tayi ram da tsohon ‘Dan shekaru 65


Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon-kasa ta gurfanar da wannan tsoho dai a gaban Kotu inda ake zargin sa da amfani da kudin bogi. Bincike ya nuna cewa kuma ba yau wannan tsoho ya shiga wannan harka ba. Da farko dai ya musanya zargin da ke kan sa.

Wannan abu dai ya faru ne jiya Alhamis a Unguwar Rigachikun da ke Garin Kaduna kamar yadda mu ka samu labari. Sunan wannan tsoho Hussaini Baba kuma yana da shekaru 65 a Duniya. Hukumar NSCDC mai kare Jama’a ta mika shi ga Jami’an EFCC na Jihar.

An samu wannan mutumi da tsabar kudi har sama da N180,000 amma duk na karya. A ciki akwai takardun N1000 da na N500 rututu. Za a cigaba da tsare wannan tsoho har wata mai zuwa kafin dai a kammala maganar bada belin sa kamar yadda Alkali mai shari’a ya bayyana



logoblog

Thanks for reading Tir: Hukumar EFCC ta damke wani tsohon kawai a Kaduna

Previous
« Prev Post

No comments:

Post a Comment